1 John 5

Bangaskiya cikin Ɗan Allah

1Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ʼyaʼyan Allah: ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3Ƙaunar Allah ita ce: a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasarar a kan duniya. 5Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

6Ga wanda ya zo ta ruwa da jini-Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta ruwa da kuma jini. Kuma Ruhu ne yake ba da shaida, domin Ruhu shi ne gaskiya. 7Gama akwai uku da suka ba da shaida: 8
Rubuce rubucen hannu na baya bayan nan na Bulget shaida a sama: Uba, Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki, waɗannan uku kuwa ɗaya ne. 8 Akwai kuma uku da suka ba da shaida a duniya: wannan (babu kalman nan a rubuce rubucen hannu na Girik kafin karni na goma sha shida)
Ruhu, da ruwa da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.
9Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. 11Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12Duk wanda yake da Ɗan yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.

Ƙarshen Magana

13Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. 14Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi saʼad da muke zuwa a gaban Allah: cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15In kuwa muka san cewa yana sauraranmu-komene ne muka roƙa-mun sani mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.

16Kowa ya ga ɗanʼuwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa adduʼa. Saboda mai adduʼan nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi adduʼa domin wannan ba. 17Dukan yin abin da ba daidai ba zunubi ne, kuma akwai zunubin da ba ya kai ga mutuwa.

18Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya yǎ cuce shi ba. 19Mun san cewa mu ʼyaʼyan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun. 20Mun kuma san cewa Ɗan Allah ya zo ya ba mu fahimta, domin mu san shi da yake na gaskiya. Muna kuma cikinsa shi wanda yake na gaskiya-cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai madawwami.

21ʼYaʼyana ƙaunatattu, ku kiyaye kanku daga gumaka.

Copyright information for HauSRK